Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta tsare wakilin jaridar LEADERSHIP na jihar, Umar Mohammed Maradun bisa dalilan da har yanzu ba a sani ba.
Ta kama Umar din ne a gidansa da ke Maradun da safiyar ranar Asabar inda jami’anta suka kai shi sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Gusau a jihar ta Zamfara tare da tsare shi a nan.
Shugabannin kungiyar ‘yan jarida NUJ da na wakilan kafafen yaÉ—a labarai na jihar Zamfara sun je sashin ofishin CID domin jin dalilan da ya sanya ‘yan sandan suke tsare dan jaridan tare da neman belin sa amma ‘yan sandan sun ki ba da belin nasa ko barin a tattauna da shi.
Jagororin ‘yan jaridan sun yi wa ‘yan sandan bitar dokar da ke cewa bai fa kamata su tsare Umar Maradun na sama da awa 24 ba, sannan sun kuma nuna mamakinsu da yadda ‘yan sanda suka ki bada belin nasa duk kuwa da cewa babu wata hujja ta zargin aikata mugun laifi.
Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Ayuba N. Elkanah ya ce zai shiga cikin lamarin domin shawo kan batun, sai dai bai yi dogon sharhi kan batun ba.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Zamfara (NUJ), Malam Ibrahim Maigari, ya hakikance kan cewa tilas a sake musu mamba, ya ce za su ci gaba da kokarinsu har sai sun tabbatar dan jaridar na LEADERSHIP ya samu ‘yancinsa.
‘Yan Jarida dai a Nijeriya na fama da kalubale iri-iri na kamu da tsarewa a duk lokacin da suka gudanar da ayyukansu da doka ta tanadar musu domin ba wannan ne na farko ba da ‘yan sanda ke tsare ‘yan jarida a sassan daban-daban ba.