A jiya Laraba ne dai rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta samu nasarar ceto Godwin Aigbogun, shugaban jam’iyyar APC na mazaba ta 9 a karamar hukumar Orhionmwon da ke jihar Edo wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Litinin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar kakakin ‘yan sanda, ASP Jennifer Iwegbu, a Benin.
- Da Dumi-Dumi: Sheikh Abduljabbar Ya Nemi A Sauya Masa Kotu
- APC Ta Gabatar Da Shettima A Matsayin Abokin Takarar Tinubu
An yi garkuwa da Aigbogun ne a hanyarsa ta komawa kauyensu daga gona a Ologbo-unu.
A cewar Iwegbu, bayan samun labarin sace shi, kwamishinan ‘yan sanda, Abutu Yaro, ya umarci jami’an rundunar ‘yan sanda ta musamman da kuma sashen yaki da masu satar mutane da su shiga cikin daji domin ceto shugaban jam’iyyar.
“Sakamakon haka, da masu garkuwar suka lura da cewa tawagar jami’an tsaro na bin su sai suka shiga rudani, inda su ka saki wanda suka sace sannan suka tsere cikin daji
“Don haka, kwamishina ya gargadi duk masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyinsu da su bar jihar ko kuma su fuskanci fushin doka domin rundunar na kan kadamin kokarin kade duk wasu masu aikata laifi a jihar.
Ta ce kwamishinan ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihan bayanai kan masu aikata laifuka da kuma ‘yan kungiyarsu.