Tsohon gwamnan Jihar Sakwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koka kan halin da siyasar Nijeriya ke ciki, yana mai cewa ‘yan siyasa a yau suna gwagwarmaya ne kadai wajen neman mukamai maimakon yin aiki don amfanin talakawa.
A wata hirarsa da BBC Hausa, Bafarawa ya yi tir da durkushewar siyasar adawa a Nijeriya, yana mai cewa ficewar fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa APC so rai ne kawai.
- Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
- Gobara Ta Ƙone Shaguna 3 Da Kayayyaki Masu Yawan Gaske A Ibadan
“Babu adawar gaskiya. Kowani dan adawa yana damuwa ne kawai game da amfanin kansa. Da zarar sun sami abin da suke so, babu sauran adawa. ”
Bafarawa, wanda ya kasance jigo a jam’iyyar PDP har zuwa murabus dinsa a ranar 13 ga Janairu, 2025, ya bayyana cewa ‘yan siyasar Nijeriya ba sa damuwa ga talakawa.
“Abin da ake kira adawa a yau shi ne kowa yana takansa ne kawai. Su tambayi kansu, ‘Me zan iya samu?’ Idan kofa daya ta rufe musa, sai su nemi wata hanyar ba tare da tsoro ko kunya ba.
“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi.
Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice.
“Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da jahilci, don haka komai yana cikin rudani,” in ji Bafarawa.
Tsohon gwamnan ya kuma nuna matukar damuwa game da karuwar jahilci a tsakanin matasa, musamman a arewacin Nijeriya, yana mai gargadin cewa makomar yankin na cikin hadari.
“Duk lokacin da kuka cusa mutane cikin jahilci ta hanyar hana su ilimi, kun gama da su. A nan arewa, a gaskiya, kusan kashi 70 cikin 100 na matasanmu ba su da ilimi. Ta yaya wata kasa ko yanki za ta ci gaba ba tare da ilimi ba?” ya tambaya.
Bafarawa ya kare talakawa masu jefa kuri’a da ke karbar kudi a lokacin zabe, yana mai cewa mawuyacin halin tattalin arziki da suke fuskanta ya sa ba su da wani zabi.
A cewarsa, taimakon Allah ne kadai zai iya ceto Nijeriya daga kalubalen da take fuskanta a yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp