Bangarorin ‘yan bindiga biyu masu hamayya da juna daga tsagin Bello Kaura da Kachalla Najaja sun yi fito na fito da juna a kusa da dajin Sunke a karamar hukumar Anka a Jihar Zamfara.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, bangarorin biyu sun shafe tsawon sa’o’i uku suna barin wuta a tsakaninsu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan ta’adda 23.
- Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Kano
- Boko Haram Na Amfani Da Na’urar Starlink Ta Elon Musk Wajen Sadarwa Ta Yanar Gizo
Kaura da Najaja, shugabannin ‘yan bindigar biyu sun yi arangama ne a dajin Sunke, inda suka yi musayar wuta.
Tsagin Kaura sun yi nasarar fatattakar yaran Najaja, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin dajin Gandu da ke yankin Bukuyum a jihar.
Wasu majiyoyi a yankin sun bayyana cewar fadan tsakanin tsagin biyu, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
Cikin shekaru hudu da suka gabata, yawancin mazauna yankin na tserewa daga kauyukansu saboda gaza biyan kudin fansa da ‘yan bindiga ke sanya musu.
Majiyoyin sun bayyana cewa Kaura na jin haushin Najaja kan kai wani hari da ya yi a yankinsa.
A wata arangama da suka yi, tsagin Kaura sun kashe ‘yan ta’adda shida daga bangaren Najaja.
Daga baya, Najaja ya tara yaransa tare da kai wa Kaura harin ramuwar gayya a dajin Sumke, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’adda 17.
Sai dai bayan wancan arangama da tsagin biyu suka yi, Kaura ya sha alwashin shafe tsagin Najaja.