Kimanin manoma 40 ne aka kashe yayin da wasu da dama ba a san inda suke ba a halin yanzu, bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai hari a garin Dumba a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Yayin da ya nemi a sakaya sunansa da yake magana kan lamarin, wani ganau wanda ya kasance daya daga cikin manoman da suka tsira daga harin, ya ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadin da ta gabata dauke da muggan makamai.
- Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)
- Masana Kimiyyar Sin Sun Samu Ci Gaba A Binciken Sarrafa Batirin Lithium
Ya ce ‘yan ta’addan kafin su fara harbe-harbe sun shaida musu cewa, har yanzu ba a janye takunkumin haramcin noma da kamun kifi a yankin ba, don haka, duk wanda aka kama a yankin ya saba wannan doka, kisa ne hukuncin shi.
Har ila yau, da ya nemi a sakaya sunansa, wani jami’in rundunar CJTF da ya taka rawa wajen ceto wadanda suka tsira, ya ce irin wadannan hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai wa manoma abu ne da ya saba faruwa, inda ya ce, a wasu lokutan, ‘yan ta’addan kan kashe kusan 10 daga cikin manoman, amma ba a cika rahoto labarin ba, amma gaskiya kalubalen da manoman ke fuskanta ya kazanta, musamman masunta a karamar hukumar Kukawa ta Jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, al’ummar Dumba na da nisan kilomita 7 zuwa fitaccen garin masunta na Baga inda ake gudanar da kamun kifi mai yawa saboda yanayin ruwan kogi da karamar hukumar ke da, kuma tana da iyaka da Jamhuriyar Chadi.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar game da harin.