Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta bayyana cewar wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe jami’anta hudu a harin kwanton bauna da suka kai a jihar.
Mazauna garin Zandam na karamar hukumar Jibia sun shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun far wa dakarun ne a ranar Lahadi.
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke KanoÂ
- Mene Ne Bambancin Ra’ayi Na Kasar Sin Dangane Da Tsarin Kasa Da Kasa ?
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Sadik Aliyu, ya bayyana cewar ‘yansanda hudu ne suka rasa rayukansu kuma tuni ta tura karin dakaru zuwa wurin.
Irin wannan harin ba shi ne na farko ba a Jihar Katsina, inda ‘yan bindiga ke kashs jami’an tsaro.
A wasu lokuta har dakarun soji suke kai wa hari.
Sai dai a baya-bayan nan rundunar sojin Nijeriya na samun nasarar kawar da jiga-jigan ‘yan bindiga a Arewa Maso Yammacin Nijeiriya.