‘Yan takarar kujerar shugaban kasar Nijeriya, a yau Alhamis sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali.
Yayin wani taro da aka yi a Abuja da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar, yayin da Kashim Shettima da ke mara wa Bola Ahmed Tinubu baya ya sanya hannu a madadinsa.
- NIS Reshen Jihar Bayelsa Ta Yi Shirin Tunkarar Zaɓen 2023
- Sin Da Argentina Sun Sha Alwashin Yayata Manufar Samar Da Al’umma Mai Makomar Bai Daya
Rashin bayyana Tinubu wajern bikin ya haifar da cece-kuce daga wasu ‘yan Nijeriya, musamman masu tsokaci a kafofin sada zumunta.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bukaci sanya hannu a kan yarjejeniyar ya lokacin bikin da aka gudanar, wajen ganin tasirinsa, a tsakanin ‘yan siyasar da kuma magoya bayannsu.
‘Yan takara 18 za su fafata domin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari wanda wa’adin mulkinsa zai kare a watan Mayu shekara mai zuwa.
A ranar 25 ga watan Fabarairu za a gudanar da zaben wanda ake sa ran mutane sama da miliyan 80 za su kada kuri’a.