Akalla mutum 25 ne suka mutu, sannan gommai suka jikkata a harin da dakarun ‘yan tawaye na RSF suka kai a sansann ‘yan gudun hijira da ke Abu Shouk da Birnin al-Fashir da ke Yammacin Sudan.
“Jami’in Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Khater ya ce mutum 25 sun mutu, sannan mutum 40 suka jikkata a harin na sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk, inda akwai kusan mutum 400,000 da suke zaman gudun hijira a sansanin,” kamar yadda jaridar Tribun mai zaman kanta a Sudan ta ruwaito a tsakiyar makon nan.
- Motocin Agaji Sun Shiga Sudan Daga Chadi A Karon Farko
- Sin Ta Yi Kira Ga Gamayyar Kasa Da Kasa Da Su Mutunta ’Yancin Kan Sudan Ta Kudu A Lokacin Mulkin Rikon Kwarya
Jaridar ta kara da cewa, “ganau sun kuma ce dakarun na RSF sun yi luguden wuta a gidajen mutane da asibitin ‘yansanda, wanda ya tilasta aka rufe asibitin.”
RSF ba ta ce komai a kan kisan ba.
An dade ana zargin kungiyar da kisan kan mai uwa da wabi a al-Fashir, inda yakin ya kashe daruruwan mutane tun bayan farkonsa a 10 ga Mayu, sannan mutane da dama suke tsere.
Watanni ke nan Al-Fashir na karkashin dakarun RSF, inda yanzu haka ake fargabar shiga karancin abinci da magunguna.
A wani labarin kuma, Ma’aikatar lafiya a Sudan ta tabbatar da mutuwar mutane 132, sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan saman da ba a taba gani ba cikin shekara guda ya haddasa a kasar.
Hukumomi sun ce ambaliyar ruwan ta shafi jihohi 10, ya yin da kusan mutum dubu 130 da yakin basasar da ake yi a kasar ya raba da muhallansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a gabashin Jihar Bahrul Ahmar, mutum 33 ne suka mutu bayan wata madatsar ruwa ta balle saboda tumbatsar da ruwan ya yi.
Ta yi gargadin adadin ka iya fin haka sakamakon har yanzu akwai wadanda suka bata ba a gano su ba.