A ranar Litinin din da ta gabata dan wasan Real Madri, Karim Benzema kuma dan kwallon tawagar Faransa ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or na kakar wasa ta 2021 zuwa 2022.
Dan wasan na Real Madrid shi ne na baya-bayan nan da ya lashe kyautar daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a bikin da yake gudana duk shekara wanda mujallar French Football kan gudanar.
Kyautar ita ce ta 66 da aka yi bikin karrama ‘yan wasan kwallon kafa da suka yi fice a duniya da aka yi a Faransa kuma a karon farko an auna kwazon dan wasa bisa bajintar da ya yi a kakar wasa, maimakon shekara daya da ake yi a baya.
Benzema ya zama na 10 da ya lashe Ballon d’Or daga Real Madrid, bayan da Luka Modric ya dauka a shekara ta 2018 daga kungiyar, bayan kuma ya taimaka wa kasar sa ta Crotia ta je wasan karshe na kofin duniya.
Tsohon dan wasan kungiyar ta Real Madrid Alfredo Di Stéfano, shi ne na farko da ya fara lashe kyautar a shekara ta 1957, sannan ya kara lashe wa a shekarar 1959, sai kuma Raymond Kopa, wanda suka buga wasa tare da Di Stéfano, shi ne ya lashe kyautar shekarar 1958 na biyu daga Real Madrid, sannan Stefanano da ya dauka karo na biyu a shekara ta 1959.
Sauran ‘yan wasan da suka lashe Ballon d’Or a Real Madrid sun hada da Zinedine Zidane a shekarar 1998, wanda ya karba daga hannun Ronaldo Nazario na Inter Milan, wanda ya lashe a 1997 da kuma a 2002, wanda ya zama zakara a Real Madrid.
Figo ya dauki Ballon d’Or a Real Madrid a shekarar 2000, sai Michael Owen a shekarar 2001 da Cannabaro a 2006 da kuma Kaka a 2007 sannan sai Cristiano Ronaldo wanda ya dauki Ballon d’Or biyar a tarihi guda hudu a Real Madrid da daya a Manchester United a 2008.
Kyaftin din tawagar Portugal wanda ke wasa a Old Trafford yanzu haka ya lashe a 2013 da 2014 da 2016 da kuma 2017.