Daruruwan ‘Yandabar siyasa sun kawo cikas a yakin neman zaben jam’iyyar APC na shiyya ta uku da yammacin ranar Asabar, a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade da ke jihar Yobe, mahaifar shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya.
An tsara aiwatar da taron gangamin yakin neman zaben ne bayan bude sabuwar kasuwar zamani wadda gwamnan jihar, Hon. Mai Mala Buni ya gina a garin Nguru, inda daga bisani aka hallara a Filin Agric da ke unguwar Katuzu a Gashuwa.
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Ahmad Lawan A Matsayin Dan Takarar APC A Yobe Ta Arewa
- Wa’adin Canjin Kudi: Buni Ya Nemi CBN Ya Ƙara Wa Jihar Yobe Lokaci
Bugu da kari kuma, tun a garin Nguru aka fara ganin alamun yiwa tawagar ‘yan siyasar ture, kana kuma kafin shiga garin da zuwa inda aka shirya gudanar da taron, wasu gungun fusatattun matasa ne suka tsaya kan hanya suna yi wa tawagar ‘yan siyasar ihu da rashin arziki akan hanya.
Abun ya kara kamari ne a lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, yake kokarin mika abin magana ga gwamna Mai Mala Buni, wanda yake tare da gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, inda kan ka ce kwabo, fusatattun matasan suka rinka shewa da ihun: ‘ba ma yi, ba ma yi, ba ma so’ tare da jifa kan mai uwa da wabi kan dandamalin da manyan baki suke tsaye a kai.
Haka zalika, an sha dage ranar da za a gudanar wannan yakin zaben a jihar, sakamakon rashin tabbas da rudanin da APC ta shiga a jihar. Al’amarin da ya samo asali daga rikita-rikitar da ta dabaibaye zaben fidda-gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar, da kuma hukuncin da kotun koli ta yanke kan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa; duk suna daga cikin abubuwan da suka tunzura wasu matasa.
Kazalika, wannan gangamin taron yakin neman zaben ya samu halartar dubun-dubatar magoya bayan jam’iyyar APC a fadin jihar, wanda ya kunshi jiga-jigan mutane, wadanda suka hada da shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, gwamna Mai Mala Buni tare da Mataimakinsa, gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya da shugabanin jam’iyyar APC a jihar Yobe da kwamitin yakin neman zaben 2023 da sauran su.