• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yang Jiechi Ya Gana Da Mai Taimakawa Shugaban Amurka Kan Harkokin Tsaron Kasa

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin tsakiyar JKS Yang Jiechi, ya gana da mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa, Jake Sullivan a Luxembourg jiya Litinin, inda suka tattauna kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwan dake jan hankulansu duka.

Yayin ganawar ta su, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, cikin ‘yan watannin da suka gabata, kasar Amurka ta rika danne kasar Sin a dukkan fannoni, lamarin ba zai iya warware matsalolin da Amurkar ke fuskantar ba, haka kuma zai jefa huldar dake tsakaninta da kasar Sin cikin mawuyacin yanayi.

  • Jakadan Sin A Saliyo Ya Halarci Taron Karawa Juna Sani Tsakanin Ofishin Jakadancinsa Da Kungiyoyin Sada Zumunta Ta Kasashen Biyu

Ya ce za a iya cewa, matakin da Amurka ta dauka bai dace da moriyar sassan biyu ba, haka kuma bai dace da moriyar sauran kasashen duniya ba. Don haka, kamata ya yi Amurka ta kara fahimtar yanayin da kasar Sin ke ciki, ta yi zabin da ya dace, ta yadda za a tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Kana Yang Jiechi ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta yarda da tsoma baki cikin harkokin gidanta ba, kuma matakan da aka dauka domin lalata dinkewar kasar Sin ba za su yi nasara ba, don haka, dole ne Amurka ta amince da ka’idar kasar Sin daya kacal a duniya, da yarjejeniyoyi uku da Sin da Amurka suka daddale. Har ila yau, dole ne Amurka ta daidaita batun dake shafar yankin Taiwan na kasar Sin ta hanyar da ta dace. Ban da haka, Yang Jiechi ya kara da bayyana matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Hong Kong da Tibet da na tekun kudancin kasar da addinai da sauransu.
Hakazalika, sassan biyu sun yi musanyar ra’ayi kan batun Ukraine da batun makaman nukiliya na kasar Koriya ta Arewa da sauransu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
Daga Birnin Sin

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Next Post
‘Kwankwaso Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023’ —Jideogu Ogbu

‘Kwankwaso Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023’ —Jideogu Ogbu

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

October 17, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.