ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda A Ebonyi Sun Damke Wasu Masoya Da Suka Sayar Da Jaririnsu A Kan Kudi N500,000

by Sadiq
3 years ago
Ebonyi

Rundunar ‘yansandan Jihar Ebonyi ta cafke wata mata ‘yar shekara 20 a duniya da kuma masoyinta da suka sayar da jaririnsu ga wani ma’aikaciyar asibiti a kan Naira 500,000.

Mahaifiyar mai suna Ola China, mai shekaru 20, a Amangwu Edda a karamar hukumar Afikpo ta Arewa a Jihar Ebonyi da wani masoyint mai suna Jonah Ogbuagu da ya mata ciki ba tare da aure ba a watan Agustan 2021.

  • Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Gargadi Gwamnati Kan Ta Inganta Ilimin Bai-Daya
  • Ministan Najeriya Ya Yi Maraba Da Kamfanonin Sin Da Su Zuba Jari A Kasar

Ola ta haifi jaririn ne a watan Afrilun 2022 a Obigbo, Ribas, inda ta je yin buya a gidan gwaggonta a lokacin da take dauke da juna biyun.

ADVERTISEMENT

Bayan ta haihu sai ta hada baki da Ogbuagu don sayar da jaririn.

Kakakin ‘yansanda a Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya bayyana a ranar Talata a Abakaliki cewa an kama ma’aikaciyar, wadda aka fi sani da “Mummy Abigail’ a Ovima, da ke karamar hukumar Afikpo ta Arewa.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

“Mummy Abigail tana gudanar da aikin karbar haihuwa a gidanta, wanda take amfani da shi a matsayin fakewa da cinikinta na haram.

“An mika wadanda ake zargin ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa domin daukar matakin da ya dace da kuma gurfanar da su a gaban kotu,” in ji SP Anyanwu.

Ya kara da cewa ‘yansanda a Ebonyi sun kuma kama wasu mutane biyu masu safarar yara, wadanda suka kware wajen sata, sace-sace, garkuwa da mutane da kuma sayar da yara.

Anyanwu ya bayar da cikakken bayaninsu da Otuu Chizaram mai shekaru 24 daga Ndukwe Akpoha da Agbi Precious mai shekaru 20 a hanyar Evuma duk a karamar hukumar Afikpo ta Arewa a Ebonyi.

“Kowanensu ya amsa laifin satar jariri,” in ji Anyanwu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Kauyuka 21 A Sakkwato

'Yan Ta'adda Sun Tarwatsa Kauyuka 21 A Sakkwato

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.