ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda A Kano Sun Gargaɗi Sarki Sanusi II Kan Fitowa Hawan Sallah

by Sulaiman
7 months ago
Sanusi

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta sake jaddada haramta duk wani nau’in hawa a yayin bikin Sallar layya da ke gabatowa. Rundunar ta nanata haramcin ne sa’o’i kadan bayan Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi, ya umurci dukkan hakimai da ke karkashin masarautar Kano da su yi taro a birnin Kano domin gudanar da bikin na shekara-shekara.

LEADERSHIP ta rahoto cewa, a ranar Talata ne Majalisar Masarautar ta fitar da wata takarda inda ta umurci hakimai da dagatai da su zo da dawakansu da mahaya a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, a shirye-shiryen gudanar da bukukuwan hawan Sallah da ake sa rai. Majalisar ta kuma shirya wani taro a ranar Alhamis 5 ga watan Yuni a fadar mai martaba da ke Kofar Kudu domin zaman kammala shirye-shiryen gudanar da taron.

ADVERTISEMENT
  • FRSC Ta Fara Binciken Hatsarin Motar Da Ya Yi Ajalin ’Yan Wasan Kano 22
  • Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya

Sai dai wata sanarwar manema labarai da rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fitar, sa’o’i kadan bayan masarautar Kano ta sanar da tsare-tsarenta, ta sake nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah, wacce ta fara aiwatar da ita a lokacin bikin Sallar Azumi da ta gabata, tana nan kuma za ta ci gaba da wanzuwa har a lokacin bikin Sallar layya ta bana.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar.

“An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da shirin wasu bata gari da masu daukar nauyinsu na yin amfani da bukukuwan hawan Sallah wajen gurgunta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda aka tabbatar a lokacin Sallar Azumi.” In ji Rundunar

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3% 

Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3% 

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.