‘Yansanda tare da dakarun Civilian Joint Task Forcez sun yi nasarar daƙile harin Boko Haram a sansanin soji da ke garin Banki, ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno.
Mazauna yankin sun yaba da jarumtar shugaban ‘yansanda na yankin, wanda ya ƙi guduwq lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari, ya kuma jagoranci kare garin.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
- Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Wasu sojoji sun tsere zuwa kasar Kamaru, amma DPO ya ƙarfafi gwiwar mutane suka tsaya su kare kansu.
Wasu majiyoyin tsaro sun ce jinkirin samun taimakon jirgin yaƙin sama ya bai wa ‘yan ta’addan damar kai farmaki da ƙarfinsu.
Duk da haka, ‘yansanda da JTF sun kare ofishin ‘yansanda da wuraren tsaron da ke kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Banki bayan harin, inda ya yaba da jarumtar mazauna garin tare da alƙawarin bunƙasa tsaro a yankin.
Zulum, ya kuma sanar da shirin sake mayar da mazauna ƙauyuka uku; Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe, sannan ya tabbatar da cewa aikin gyaran hanyar Banki ya an fara shi.
Ya buƙaci matasa su yi rajistar katin zaɓe, tare da jan hankalin ‘yan kasuwa su haɗa kai da jami’an tsaro domin ɗorewar zaman lafiya.














