Kwamishina mai kula da tsugunar da ‘Yan gudun hijira na jihar Borno, Engr. Ibrahim Idris Garba, ya rasu.
Kwamishinan ya rasu ne a safiyar ranar Asabar a gidan baki da ke rukunin gidaje 777 a Maiduguri babban birnin jihar.
- Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Jihar Borno
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Lalata Baburansu 40 Da Bindigu 6 A Borno
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta fara gudanar da binciken gaggawa kan musabbabin mutuwar kwamishinan.
Mai magana da yawun Gwamna Babagana Umara Zulum, Malam Isa Gusau, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.
Gusau ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ziyarci gidan da Engr. Garba ya rasu a Maiduguri ranar Asabar.
Gwamna Zulum ya bayyana alhininsa tare da iyalan marigayi kwamishinan da sauran masoya da abokan arziki da ‘yan majalisar zartarwar jihar Borno.
Marigayi Engr Ibrahim Idriss Garba a lokacin rayuwarsa ya taba zama mai baiwa gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman kafin daga bisani a nada shi kwamishinan sake tsugunar da’Yan gudun hijira.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa kwamishinan kurakuransa, ya shigar da shi Aljanna madaukakiya.