Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Kwamishina CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ta samu nasarar ƙwato bindigu da kayan miyagun laifuka a ƙaramar hukumar Anka, bayan fafatawa da ‘yan bindiga.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ne, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, a ranar 24 ga watan Afrilu, 2025 da misalin ƙarfe 7 na safe.
- Dalilin Nijeriya Na Kulla Yarjejeniya Da Kasar Sin Kan Noman Rake
- An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
Tawagar ‘yansanda ƙarƙashin ASP Bilyaminu Koko, sun yi sintiri a hanyar Bobo zuwa Mayanchi, inda suka yi arangama da ‘yan bindigar.
A yayin artabun, ‘yansanda sun yi nasara, inda ‘yan bindigar suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Bayan haka, ‘yansanda sun ƙwato; sabuwar bindiga ƙirar AK-47 mai lamba 20746, tabar wiwi da ake zargin daga ƙasar Indiya ne.
Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro.
Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka.
Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira idan aka ga wani abu da ba a gamsu da shi ba; 08034805544, 07032490813 da kuma 09053872244
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp