Kwamishinan ‘yansandan Jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya bayar da tabbacin tsaro ga masu yi wa kasa hidima na jihar.
Kwamishinan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci sansanin horar da masu yi wa kasar hidima na wucin gadi a makarantar kimiyya da ke Gusau, babban birnin jihar.
- 2023: Kwankwaso Na Shan Matsin Lamba Kan Yi Wa Atiku Mubaya’a
- Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 500 Don Biyan Giratuti
“Ziyarar ita ce don ingantawa da kuma karfafa tsare-tsaren tsaro da ake da su a sansanin da nufin tabbatar da tsaro ga dukkan masu son yi wa kasa hidima a jihar nan,” in ji shi.
Kwamishinan a jawabin da ya yi wa masu yi wa kasar hidima, ya tabbatar musu da kudurin ‘yansanda na kare rayukansu a sansanin da kuma wuraren da suka fi daukar nauyi.
Malam Yusuf ya kara da jan hankalinsu da su kasance masu lura da kansu tare da kai rahoto ga ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa.