Rundunar ‘yansanda a jihar Yobe ta sanar da cafke wasu kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, wadanda suka addabi kananan hukumomin Dapchi da Tarmuwa a jihar.
A cikin sanarwar manema labaru mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce jami’ansu sun yi nasarar kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane a ranar 9 ga Afrilun 2025.
- Daga Yau Sin Ta Fara Karbar Karin Haraji Na 84% Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Daga Amurka
- Barcelona Ta Kama Hanyar Lashe Gasar Zakarun Turai A Karon Farko Bayan Shekaru 10
Ya ce, wadanda ake zargin su ne Babaro Baushe, dan kimanin shekaru 40 tare da Umaru Dau’a mai shekara 25, dukansu yan asalin kauyen Askuwari ne a karamar hukumar Tarmuwa.
SP Abdulkarim ya kara da cewa, “Jami’an ‘yansanda na yankin Dapchi ne suka yi nasarar kama su yayin wani samame da suka kai a ranar Laraba da misalin karfe 5:00 na safe”.
Wadanda ake zargin su na da alaka da aikata manyan laifuka da dama, ciki har da wani harin da suka kai a kauyen Badegana a ranar 21 ga Nuwamba, 2024, a gidan wani mutum, inda suka kashe mutum daya.
Har ila yau, a ranar 10 ga Maris, 2025, sun yi wa wani mutum mai suna Kudi Ibrahim, a kauyen Askuwari, a karamar hukumar Tarmuwa, barazanar garkuwa dashi ko su kashe shi, hakan suka tilasta masa dole ya basu Naira 250,000.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa rundunar ‘yansandan hadin kai tare da ba su bayanai masu inganci kan bata-gari da masu aikata manyan kaifuka a jihar akan lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp