Rundunar ‘yansandan Jihar Yobe ta cafke wani yaro dan shekara 16 bisa zarginsa da cin mutuncin gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, kafar sada zumunta.
An kama yaron ne a ranar 11 ga Disamba, 2022, amma ba a gano hakan ba sai a ranar Litinin.
- Tsare Okupe Ba Zai Hana Ni Zama Shugaban Kasa A 2023 Ba – Peter Obi
- 2023: Ba Zamu Hade Da Kowace Jam’iyya Ba – Idahosa
A ranar Litinin ne mahaifin yaron mai suna Garba Isa ya ja hankalin jama’a kan halin da dansa ke ciki, ya kuma roki hukumar ‘yansanda da ta sake shi.
An tattaro cewa an kama matashin ne a garin Nguru na jihar, daga bisani kuma aka mayar da shi sashen bincike na rundunar ‘yansandan jihar da ke Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
A wata hira da maihaifin yaron da LEADERSHIP ta yi a Damaturu, Isa wanda mai wanki da guga ne, ya yi Allah wadai da matakin da dansa ya dauka.
Ya roki gwamnan da ‘Yansanda da su tausayawa dan nasa su sake shi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa ‘yansandan na shirin gurfanar da matashin zuwa kotu bayan bincike.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, kwamishinan ‘yansandan jihar, ya amince cewa wanda ake zargin yana tsare, inda ya ce idan aka kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.
“Idan muka kammala bincikenmu, tabbas za a gurfanar da shi a gaban kotu.
“Mutane suna amfani da kafafen sada zumunta wajen zagi da bata wa mutane mutunci, akwai bukatar a tsaftace al’umma, “in ji shi.
Ya kara da cewa, “Ba za ku iya amfani da shafukan sada zumunta ba, ku fara yada abubuwa iri-iri, akwai doka da oda a Nijeriya, duk wanda ya taka hakkin wani za a hukunta shi.”