Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Isaac Idahosa ya yi watsi da yiwuwar hadewa da wasu jam’iyyun siyasa gabanin zaben 2023 amma ya ce jam’iyyarsa a bude take ga masu son shigarta.
Idahosa ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, inda ya kara da cewa NNPP na da yakinin samun nasara a zaben da za a yi a watan Fabrairun 2023.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 40 A Zamfara
- An Amince Da Kudurin Aiki Na Kunming-Montreal Game Da Kare Mabambantan Halittu Yayin Taron COP15
“Ko da yake wasu jam’iyyu ne ke son yin hadaka da NNPP, ba wai mu ne muke kokarin yi ba.
“Hadewar ta kare tun baya ba tare da cimma matsaya ba kamar yadda kuka sani. Ga wadanda suke ganin ya dace su shiga tafiyarmu, kofa a bude take, mu yi wa juna adalci, mu hada kai don ganin mun samar da gwamnati mai nagarta wanda abin da muke shirin yi ke nan.” in ji shi.
Idahosa, wanda Bishop ne a Legas, ya kuma ce jam’iyyar NNPP ta samu karbuwa sosai a fadin kasar nan, musamman a matakin kasa.
Abokin takarar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa Nijeriya za ta inganta idan ta samu aka samu shugaba na gari.