Rahotanni sun bayyana cewa wata budurwa ta mutu a yayin da ta ke tsaka da yin lalata da saurayinta wanda mai sana’ar aski ne a garin Ilorin na jihar Kwara.
Rundunar ‘yansandan jihar ta ce ta kama saurayin marigayiyar kan lamarin.
- An Kashe Basaraken Taraba, An Sace Matarsa, Dansa Da Wasu 8
- Hukuncin Kotun Ƙoli: APC Ta Nemi Atiku Ya Yi Haƙuri Ya Rungumi Ƙaddara
LEADERSHIP ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a unguwar Temidire da ke yankin Offa Garage a Ilorin.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mai askin ya sha kwayoyin kara kuzari ne don kece raini a wajen budurwarsa yayin jima’i.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP cewa, “An ce yarinyar ta gaji da jima’in wanda ya hakan kai ga rasa rayuwarta.
Majiyar ta ce saurayin matashiyar ya ja hankalin mutane bayan da ta sume.
An garzaya da ita zuwa wani asibiti da ke kusa, inda aka tabbatar da mutuwarta.
An kuma tattaro cewa a mamallakin wurin da lamarin ya faru ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yansanda na Ilorin, daga bisani aka kama matashin mai matsakaicin shekaru.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce “Rundunar ‘yansandan jihar ta kama wanda ake zargi yayin da aka fara gudanar da bincike domin sanin hakikanin abin da ya faru tsakaninsu.”