Rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa ta cafke wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke jihar Nasarawa bisa zarginsa da kashe abokinshi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO), SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a garin Lafia babban birnin jihar.
- Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi?
- Saudiyya Ta Yi Watsi Da Shirin Fitar Da Falasdinawa Daga Gaza
Ya ce kamen ya biyo bayan korafin da wata mata mai suna Madam Mercy Bassey ta yi game da wani rikici da ya barke tsakanin wani mai haya a gidanta da abokinsa.
Ya ce, bayan wannan korafin, an aika jami’an tsaro zuwa wurin, inda suka gano Ibrahim Matthew, dalibin ND2 na bangaren Kwamfuta, kwance cikin jini.
SP Nansel ya ce an garzaya da dalibib zuwa babban asibitin garin Nasarawa amma ya mutu sakamakon munin raunin da ya samu.
SP Nansel ya ce wanda ake zargin, John Gambo, dalibin bangaren karatun aikin banki (ND2) da kuma sarrafa kudi, ya shiga hannu kuma ya amsa laifin daddatsa abokinshi da gatari da wuka.
Jami’in ya kara da cewa, an kwato makaman da ya yi amfani da su wajen kai harin dauke da jini wanda hakan zai zama cikakkiyar shaida.