Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta cafke wani matashi mai suna Munkaila Ahmadu mai shekara 37 a kauyen Zarada-Sabuwa da ke Karamar Hukumar Gagarawa a Jihar Jigawa bisa zargin kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da tabarya.
Da yake tabbatar da kamun a ranar Alhamis, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce wanda ake zargin ya yi amfani da wata tabaryaz inda ya doke iyayen nasa har lahira.
- Buhari Ya Nada Sirikinsa Shugaban Kamfanin Buga Kudi Na Kasa
- Za Mu Taimaka PDP Ta Fadi Zaben 2023 -Wike
Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 1 ga Satumba, 2022 da misalin karfe 12 na rana.
Kakakin ‘yansandan ya bayyana cewa, da samun bayanai kan faruwar mumunan lamarin, ‘yansanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gumel inda aka tabbatar da mutuwarsu.
Ya bayyana sunayen wadanda aka kashen da Ahmadu Muhammad mai shekara 70 da Hauwa Ahmadu mai shekara 60.
“Sai dai wasu mutane biyu da ake zargin sun jikkata a yayin faruwar lamarin, Kailu Badugu da kuma Hakalima Amadu duk a kauyen Zarada-Sabuwa, karamar hukumar Gagarawa.
“Binciken farko ya nuna cewa, Ahmad Muhammad da Hauwa Ahmadu sun kasance iyayen wadanda ake zargin ne,” in ji kakakin.
Ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aliyu Sale Tafida, ya bayar da umarnin a mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse domin gudanar da bincike na tsanaki.