Rundunar ‘Yansandan jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a wana samame suka gudanar a jihar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘Yansandan jihar, Lawal Shiisu, ya fitar a ranar Laraba a Dutse, ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin wadanda ake zargi da laifin fashin wani direban babur.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Yi Wa Jama’a Kutse A Asusun Banki
- Jami’an Tsaro Sun Yi Kwanton Bauna Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji 10 A Kaduna
Ya ce wanda abin ya ritsa da shi, Ashiru Musa, na kauyen Kyran, ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yansanda na Fanisau.
Marigayin ya bayyana cewa ‘yan bindigar biyu dauke da makamai ne suka tare shi inda suka tafi da babur dinsa mai lamba AYE 918 UP Ogun.
Shisu ya ce, ‘yan sintiri da ke aiki a yankin Fanisau sun yi kokarin bin sawun ‘yan fashi da makamin inda suka samu nasarar kwato babur din.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana sunayensu ‘yan Fashin da suka hada da Tijjani Haruna mai shekaru 19 da kuma Baballe Abdulrahman mai shekaru 25.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga na karamar hukumar Ringim sun kuma kama wasu mutum uku da ake zargi.
Wadanda ake zargin su ne, Ahmadu Audu da Shuaibu Bayeri da kuma Samaila Musa, wadanda suka fito daga kauyen Majiyar Kirdau a karamar hukumar Ringim, an kama su ne bisa laifin hada baki, fashi da makami da kuma haddasa munanan raunuka.
Shiisu ya ce, wadanda ake zargin sun amsa laifin sace babura da dama a karamar hukumar Ringim da kewaye.
Ya kara da cewa, “Sun kuma ambaci wasu gungun ‘yan bindiga da kuma wanda suke taimaka musu a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.”
Shiisu ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.