Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta ce ta kubutar da masu yi wa kasa hidima (NYSC) 15 da wasu ‘yan bindiga suka sace a jihar.
An tattaro cewa masu yi wa kasa hidimar na kan hanyar zuwa Legas ne bayan shirin wayar da kansu na tsawon makonni uku a yankin Ihiala da ke jihar.
- Shugabar Matan NNPP Reshen Abuja Ta ‘Yanta Fursunoni 4
- NUC Ta Daga Darajar Kwalejin Ilimi Ta Sa’adatu Zuwa Jami’ar Ilimi Ta Kano
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da ceto mutanen a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Tochukwu, ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da masu yi wa kasa hidimar.
Ganin yadda jami’an ‘yansandan suka kutsa cikin daji, ya sa ‘yan bindigar suka tsere suka bar wadanda suka sace.
“Jami’an ‘yansandan Jihar Anambra, da misalin karfe 11:15 na safiyar yau, 14/2/2023, suna amsa kiran gaggawa a kan hanyar Isseke, Ihiala, sun ceto masu yi wa kasa hidima 15 da aka sace daga sansanin NYSC na Eziama-Obaire, a Karamar Hukumar Nkwerre Jihar Imo.
“Bayanai sun nuna cewa matasan sun kammala shirin wayar da kan jama’a na tsawon makonni uku a yau, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Legas, wanda daga bisani aka sace su a mahadar Ihiala, da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi.
“An dauke motarsu zuwa Isseke, babbar titin Ihiala-Orlu inda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.”