Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ce ta ceto matafiya 76 da aka yi garkuwa da su a hanyar Funtua zuwa Zaria a unguwar Gulbala a karamar hukumar Giwa ta jihar, ta hanyar hadin gwiwa da sojoji.
Kakakin rundunar ‘yansandan, DSP Mohammed Jalige, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Juma’a, bayan rahoton da aka samu daga hedikwatar ‘yansanda a karamar hukumar Giwa.
- Xi Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Ilimi Karo Na 16 Na Cibiyoyin Kimiya Na Kasashe Masu Tasowa
- Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Taron MDD Da Sin Kan Huldar Kasa Da Kasa Game Da Binciken Sararin Samaniya
A cewarsa, rundunar ‘yansandan ta samu rahoton ‘yan bindiga da dama ne suka tare hanya, kuma a cikin haka ne suka yi awon gaba da fasinjoji da dama, zuwa inda suke.
Ya bayyana cewa, rundunar ta tattara jami’an tsaro ciki har da sojoji, inda suka shiga wurin, inda suka gano wata motar da babu kowa a ciki – wata motar kirar Ford mai dauke da lamba APP 667 XG, ta ce ta dauki fasinjojin da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce sojojin sun kara tarwatsa duk wani shingen hanya, tare da yin artabu da ‘yan bindigar tare da samun nasarar ceto dukkan mutane 76 da lamarin ya rutsa da su.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda abin ya rutsa da su a cikin motar sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato zuwa wurare daban-daban, yayin da barayin suka tare su,” in ji shi.
A cewarsa, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aiki a yankin gaba daya domin neman babban direban babbar motar dakon kaya da wasu fasinjoji biyu da har yanzu ba a kai ga tantance su ba.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Yekini Ayoku, wanda ya bayyana jin dadinsa kan hadin kai tsakanin jami’an tsaro a jihar, ya alakanta wannan nasarar da kokarin da ‘yansanda da sojoji suka yi, kamar yadda ya ba jama’a tabbacin ci gaba da samun nasara a kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.