Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ceto wasu mutum hudu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina
- ‘Yan Fashin Daji Na Cin Karensu Ba Babbaka A Jihar Katsina
Aliyu ya ce, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Katsina, rundunar ‘Yansanda tare da hadin guiwar sojojin Nijeriya sun ceto mutane hudun da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a fadid jihar.
Kakakin ‘Yansandan ya jaddada cewa, sun gudanar da aikin kubutar da mutanen ne yayin aikin sintiri da suke gudanarwa kullum a kauyen Dankolo, karamar hukumar Dandume da ke jihar.
“A yau, 28 ga Oktoba, 2023, da misalin karfe 08:30 na safe, rundunar hadin guiwar ‘Yansanda da jami’an soji sun yi nasarar kubutar da mutum hudu wadanda aka yi garkuwa da su.” Cewar Kakakin ‘Yansanda.
Rundunar ‘Yansandan jihar ta bukaci al’ummar jihar da su bayar da hadin kai wajen kai rahoton duk wani abu da suka samu ko wani mutum zuwa ofishin ‘yansanda mafi kusa.