Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta ce ta ceto wasu mutane biyar da aka sace tare da tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane a Jihar Kebbi.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa a ranar 27 ga watan Yuli, 2025, wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari garin Sangara a karamar hukumar Shanga, inda suka sace mutum uku.
- Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha
Waɗanda suka sace sun haɗa da Muhammad Namata, Gide Namata da Hamidu Namani.
Sai dai jami’an tsaro tare da ‘yan sa-kai sun bi sahunsu zuwa tsaunukan Shanga, inda suka yi musayar wuta da su.
Masu laifin sun tsere cikin daji da harbin bindiga, sannan an ceto mutanen uku.
Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade.
Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu.
‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp