Rundunar ‘Yansanda Jihar Kebbi ta yi nasarar hana wani yunkurin sace mutum, inda ta ceto wani da aka yi garkuwa da shi daga hannun ‘yan bindiga a Kauyen Kesan, Karamar Hukumar Shanga.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa lamarin ya faru da safiyar Asabar lokacin da ‘yan bindiga suka afka cikin al’umma suka sace wani matashi mai shekara 25, Abdulmumini Alhaji Ahmadu.
- An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
- NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano
“Bayan samun kiran gaggawa, Dibisional Police Officer na Shanga ya hanzarta hada tawagar ‘yansanda da ‘yan sa-kai, inda suka bi sahun masu garkuwa da mutane har cikin daji.
“A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar.
An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki.
Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi.
“Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu fadakarwa tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci, domin hana aikata laifuka.
Kwamishinan ya jaddada cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, yana mai bayyana cewa hadin kai mai karfi tsakanin jami’an tsaro da jama’a shi ne ginshiki wajen kawo karshen ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga zaman lafiya a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp