A ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar Imo da ke Owerri, babban birnin jihar.
Sai dai jami’an ‘yansandan da ke bakin aiki a wurin sun fatattaki maharan tare da bindige uku daga cikinsu.
Majiyoyi sun ce maharan sun fara harbe-harbe a wurin ne da misalin karfe biyu na dare tare da jefa kananan bama-bamai da aka hada na hannu, lamarin da ya lalata wasu sassan hedikwatar kamin jami’an ‘yansandan su kawo dauki.
An kwato motoci da bindigogi da na’urorin sadarwa daga hannun maharan.
Cikakkun bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp