Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102.
Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an kama su ne a ranar 10 ga watan Afrilu a unguwar Dorayi Babba da ke jihar, sakamakon wani hadin gwiwa da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano suka jagoranta.
- Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
- Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gudanar da aikin ne bisa wani sahihan bayanai da suka kai ga gano tarin haramtattun makaman.
Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yaba da matakin gaggawar da jami’an suka dauka tare da jaddada aniyar rundunar na dakile yaduwar makamai marasa lasisi a fadin kasar nan.