Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da aikin sake gina babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano, wacce hanya ce mai muhimmanci ga ci gaban rayuwar al’umma da tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.
Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ba kamfanin Julius Berger aikin hanyar amma gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta soke kwangilar ta mika ta ga wani kamfani saboda tafiyar wahainiya da aikin ke yi wanda a karshe ya tsaya cak.
- Yawan Jigilar Kayayyakin Da Aka Yi Ta Layin Dogo Na Sin Ya Karu A Rubu’in Farko
- Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
Sai dai an kammala wasu sassan hanyar.
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas.
A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Sani ya bayyana cewa, an yi biris da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin.
Sai dai Gwamnan ya kafa uzurin cewa, baya ga kudade, rashin tsaro da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin ne kamfanin Berger ya ki zuwa wurin domin ci gaba da aiki.
Amma a yanzu, hanyoyin da aka bi na magance matsalar tsaro yana haifar da sakamako mai kyau, domin masu ababen hawa na iya bin hanyar ba tare da fargabar an kai musu hari ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp