Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Borno sun gano wata nakiya da bata tashi ba a wata gona da ke karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, ASP Nahum Daso, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, rundunar ta samu rahoton ne daga wani Babagana Kachalla, wanda ya ce, ya ga wani abu da yake zargin nakiya ce a gonarsa.
ASP Daso ya ce, bayan samun wannan labari, kwamishinan ‘yansanda na jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya tura kwamandan bincike da warware nakiyoyi da ke sansani na 13, Maiduguri, tare da tawagarsa, zuwa wurin da aka gano nakiyar.
Daso ya kuma tabbatar da cewa, an warware nakiyar cikin nasara ba tare da wata matsala ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp