Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta gargadi jam’iyyar NNPP da jam’iyyar adawa ta APC da su janye zanga-zangar da za su yi a ranar Asabar.
Rundunar ‘yansandan ta yi barazanar za ta saka tsinke da duk wanda aka kama a yayin gudanar da zanga-zangar.
- Kasuwancin Zamani Na Kasar Sin Ya Samu Babban Ci Gaba A Shekarar 2022
- Samar Da Ci Gaba A Bangaren Ma’adinai: Ministan Yaɗa Labarai Ya Yaba Da Koƙarin Takwaransa Na Ma’adinai
Idan dai ba a manta ba jam’iyyun NNPP da APC ne suka hada magoya bayansu domin shirya zanga-zanga a ranar Asabar, domin bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a baya-bayan nan, wadda ta tsige gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.
A halin da ake ciki, matakin da bangarorin biyu suka dauka tun bayan sanarwar, ya haifar da fargaba a zukatan mazauna jihar kan zanga-zangar da aka gudanar Laraba wadda ta haifar da yamutsi.
Sai dai a wata sanarwar da kwamishinan ‘yansandan jihar Mista Husaini Gumel, ta hannun kakakin rundunar SP. Haruna Kiyawa ya yi gargadi masu shirin shiga zanga-zangar.
Don haka sanarwar ta bayyana cewa, “bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yi kira ga daukacin mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani nau’in taro, zanga-zanga don gujewa hargitsi.