Bayan daure wani mutum mai shekaru 67 mai suna Ibrahim Ado da aka yi a wani gida da ke a kan titin Bayajidda daura da titin Ibrahim Taiwo a karamar hukumar Kaduna ta Arewa har na tsawon shekaru 20, rundunar ‘yansanda jihar, ta gayyaci mutane biyar don su taimaka mata ta gudanar da bincike kan lamarin.
An ruwaito cewa, an gano mutumin ne a gidan a ranar Laraba a daure kuma kulle a cikin wani dakin.
- Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Nnamdi Kanu, Ta Kalubalanci Hukuncin Babbar KotuÂ
- An Yi Wa Manoma 5 Yankan Rago A Wani Sabon Rikici A Benuwe
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Mohammed Jalige ne, ya bayyana wa manena labarai hakan a gidan da aka gano mutumin, inda ya ce, jami’an kiwon na duba gari ne suka kawo rundunar rahoton lamarin.
Ya ce, bayan karbar rahoton, Kwamishinan ‘yansanda Yekini Ayoku, ya umarci DPO din ‘yansanda mai kula da Magajin Gari da ya tura jami’an ‘yansanda zuwa gidan, inda suka kubutar da mutumin.
Ya ce, Kwamishinan ya kuma bayar da umarnin a samo bayanai daga wurin mutanen da ke makwabta da gidan tare da gudanar bincike.
“Da muka je gidan mun iske mutumin tsirara, inda muka ba shi wasu kaya ya sanya.
“Mun fahinci cewa, mutumin na da ‘ya’yan da matarsa wadanda ba a san inda suke ba a yanzu.”
Kakakin ya ce, Kwamishinan ya kuma bayar da umarnin a kai shi asibiti don duba lafiyarsa.