Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi kan zargin karya dokar da ta haramta Hawan Sallah a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce rundunar ta jaddada cewa babu wanda zai karya wannan doka ba tare da hukunci ba.
- Sabbin Motocin Bas 100 Masu Aiki Da Lantarki Sun Fara Jigilar Fasinjoji A Birnin Addis Ababa
- Rundunar PLA Ta Kaddamar Da Atisaye A Yankunan Tsakiya Da Kudancin Zirin Taiwan
Tun kafin Sallah, ‘yansanda sun sanar da haramta Hawan Sallah a Kano, inda suka ce sun samu bayanan sirri na yiwuwar wasu ɓata-gari za su haddasa rikici yayin hawan.
Haka kuma, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kafa wani kwamiti na ‘yansanda takwas domin binciken rikicin da ya faru a ranar Sallah yayin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke komawa gida bayan Sallar Idi.
A lokacin wannan hatsaniya, an kashe wani jami’in tsaro tare da jikkata wani daga cikin masu tsaron tawagar sarkin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp