Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano, ta sanar da haramta hawan Sallah a lokacin bukukuwan Ƙaramar Sallah mai zuwa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne, ya bayyana haka a yayin taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke birnin Kano.
- Dalilin Da Ya Sa Ɗanyen Man Da Ake Haƙowa A Ribas Ya Ragu
- Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
Ya ce an ɗauki matakin ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ana shirin tayar da fitina yayin hawan.
“Wannan mataki ya zama dole bayan tattaunawa da hukumomin da suka dace, domin bayanan sirri sun nuna cewa wasu da aka ɗauka haya za su fake da hawan domin haddasa rikici,” in ji shi.
Sai dai wannan umarni ya saɓa wa ƙudirin Gwamnan Kano wanda ya buƙaci dukkan masarautu su shirya hawan.
Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin.
Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke shirinsa na yin hawan, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da malamai da dattawa suka ba shi.
“Muna tabbatar muku cewa hawan Sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai haddasa tashin hankali, wajibi ne a dakatar,” in ji Aminu Ado Bayero.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp