Rundunar ‘Yansandan Jihar Gombe ta bayyana cewa ta kwato tarin miyagun kwayoyi bayan wata nasarar samame da ta kai a maboyar ‘yan ta’adda da ake zargi, da ke bayan wani katafaren kanti na ‘Gombe Local Government Shopping Complex’.
Wannan bayani ya fito a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na ‘yansanda, DSP Buhari Abdullahi, ya sanya hannu a kai.
- Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul
- JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i
Abdullahi ya ce an gudanar da samamen ne ta hannun jami’an ‘yansanda na sashen Gombe yayin wani aikin yau da kullum na fatattakar wuraren da aka tabbatar da ayyukan laifi a yankin.
Ya bayyana cewa a ‘yan watannin da suka gabata, rundunar ta kara kaimi wajen kai samame a wuraren da ake zargin yin laifuka a fadin jihar, a wani bangare na kokarinta na rage yawan shan miyagun kwayoyi da laifukan da suka shafi hakan, wadanda hukumomi ke cewa sau da dama su kan zama sanadin tashin hankali da aikata laifuka musamman tsakanin matasa.
“Lokacin da barayin suka hango tawagar sintiri na kusantowa, sai suka tsere, suka bar tarin miyagun kwayoyi da wasu haramtattun abubuwa a wurin,” in ji Abdullahi.
Mai magana da yawun rundunar ya lissafa abubuwan da aka kwato da suka hada da kwayoyin “Suck and Die,” Tramadol da Diazepam, inda ya ce an kwashe su gaba daya zuwa ofishin ‘yansanda domin ci gaba da bincike da daukar matakan da suka dace.
“Dukkan shaidun da aka kwato an tafi da su ofishin ‘yansanda, kuma bincike na ci gaba domin gano da kama wadanda suka tsere,” in ji shi.
Kwamishinan ‘yansanda, CP Bello Yahaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen bisa gaggawa da kwarewa, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da laifuka da shan miyagun kwayoyi a Jihar Gombe.
“Rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa Gombe ta kasance jiha marar laifi da kuma marar miyagun kwayoyi,” in ji shi.
“Muna aikawa da gargadi mai karfi ga duk masu aikata laifuka da su daina duk wani nau’i na aikata laifi ko kuma su fuskanci fushin doka,” in ji CP Yahaya.
Ya kuma roki jama’a da su ci gaba da bin doka da oda tare da taimaka wa ‘yansanda da sahihan bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
“Muna kira ga al’umma da su rika sanar da ofishin ‘yansanda mafi kusa idan sun ga wani motsi ko aiki da suke shakka domin a dauki mataki cikin gaggawa,” in ji sanarwar.
A watan Afrilu, Rundunar ‘Yansandan Jihar Ogun ta gudanar da aikin tsaro na tsawon sa’o’i biyu a Sagamu Interchange bayan samun rahoton wani harin ‘yan fashi da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum a kan hanyar Lagos–Ibadan Expressway.
A cewar rundunar, kwamishinan ‘yan sanda Lanre Ogunlowo ne ya jagoranci duba wurin, inda aka gano haramtattun kasuwanin, ‘yan daba da kuma maboyar ‘yan ta’adda a cikin dazukan da ke kusa da wurin.
A lokacin aikin tsaron, an kama mutum uku da ake zargi, sannan kuma an kara tsaurara sintiri a yankin domin hana sake kai irin wannan hari a nan gaba.