‘Yansanda a Jihar Nasarawa, sun kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto wasu ɗalibai biyu da aka sace a jihar.
An kama wanda ake zargin ne bayan da aka samu kiran gaggawa a ranar Lahadi cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari yankin.
- Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts
- Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Shetima Jauro Mohammed, ya gaggauta tura jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane domin bin sahun miyagun.
Bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaro sun kai samame a ranar 1 ga watan Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a dajin da ke bayan 500 Housing Unit a kan titin Doma, a Lafia.
A lokacin samamen, ‘yansanda sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen.
Da suka ga cewa ba za su yi nasara ba, sai suka tsere suka bar waɗanda suka sace.
An kama mutum ɗaya, Ibrahim Musa, mazaunin ƙauyen Abuni a Ƙaramar Hukumar Awe.
Ya ya bayar da muhimman bayanai da ke taimakawa wajen bincike.
Kwamishinan ya jinjina wa jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane bisa ƙoƙarinsu kuma ya jaddada aniyar ‘yansanda na yaƙi da aikata laifuka.
Ya buƙaci jami’ansa da su ci gaba da jajircewa don tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp