Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wani Darakta Abubakar Gambo da ke aiki a ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da kadarorin gwamnati.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Hussaini Gumel ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Talata.
- Hukumar Ilimi A Matakin Farko Ta Kaduna Ta Fara Horas Da Malamai 8,500 Fasahar Kwamfuta A Fadin Jihar
- MDD Za Ta Sake Shirya Taron Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza
Gumel ya ce, an kuma kama wani mataimakin sakatare, Baba Yahaya da wani tsohon Manajan kamfanin Karefa Irrigation Scheme a karamar hukumar Tudun Wada.
An kama su ne bisa zarginsu da rubuta jabun wasika da ta ba da izinin yin gwanjon wani babban fanfunan ruwa da tanki, wanda aka ce, kayan na daga cikin muhimman abin amfani jama’a.
Gumel ya bayyana cewa, kin amincewar da Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Ali Makoda ya yi game da takardar, ya tabbatar da cewa, ba da izinin yin gwanjon kayayyakin, ba gaskiya ba ne yaudara ce tsantsa.
Gumel ya ce, ana kan bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.