Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, sun kama wani kasurgumin dan fashi ake zargi da aikata fashin makami, tare da kwato bindigu biyu kirar AK-47 da alburusai 47.
Kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa, ya ce a ranar Talata aka kama wanda ake zargin, Hassan Iliya, mai shekaru 35, yayin da yake kokarin tserewa a kan babur.
- Gwamnatin Kano Ta Sake Sassauta Dokar Hana Fita
- Zanga-zanga: Tinubu Bai Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki Ba – PDP
A ranar 5 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 2 na dare, wani mazaunin garin Yandadi a karamar hukumar Kunchi a Jihar Kano, ya kai rahoton cewa ‘yan fashi sun kai masa hari a gidansa kuma sun sace masa kudi har Naira miliyan 15.
Duk da zanga-zangar da ake yi, Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo Garba, ya umarci wata tawaga ta musamman domin kamo ‘yan fashin.
Da misalin karfe 6 na safiyar wannan rane ne, tawagar ta kama Hassan Iliya a garin Alhazawa a Jihar Katsina yayin da yake kokarin tserewa a kan babur.
Sun samu bindigu biyu kirar AK-47, alburusai 47, da kuma Naira miliyan biyar a jakarsa.
Kwamishinan ‘yansandan ya yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abun zargi.