Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa, ta kama mutane 153 a wani samame da aka kai don yaƙi da miyagun laifuka da shaye-shaye a faɗin jihar.
‘Yansanda sun ce an kama mutanen ne da laifin sayarwa ko mallakar miyagun ƙwayoyi.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
- Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
A lokacin samamen da aka gudanar a sassa 42 na rundunar, an ƙwato ƙwayoyi sama da 13,000, babur guda ɗaya, da kuma kuɗi har Naira 228,570.
Ƙwayoyin da aka samu sun haɗa da Tramadol, Exol, D5, da kuma tabar wiwi.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’ansa bisa jajircewarsu, inda ya kuma buƙaci jama’a su riƙa ba da bayanai masu amfani domin taimaka wa yaki da laifuka.
Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.