• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano

by Sadiq
4 months ago
Kano

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta kama matasa 51 da ake zargi da addabar jihar da faɗan daba. 

Haka kuma ta ƙwato makamai masu hatsari da miyagun ƙwayoyi a yayin wani samame da ta kai na tsawon kwana uku a sassa daban-daban na birnin Kano.

  • Hada-hadar Tattalin Arzikin Sin Ta Gudana Bisa Daidaito A Watan Mayu
  • Sarkin Musulmi Ya Nuna Baƙin Ciki Kan Kisan Kiyashi A Binuwe

An gudanar da samamen ne daga ranar Juma’a, 13 ga watan Yuni, zuwa Lahadi, 15 ga watan Yuni.

‘Yansanda sun mayar da hankali wuraren da aka fi samun aikata laifi a ƙananan hukumomin Birni, Dala, Gwale, da Tarauni.

Sauran sun haɗa da unguwannin Kofar Mata, Zage, Kurna, Rijiyar Lemo, Dorayi, Hotoro da Sheka.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

DSP Hussaini Abdullahi, Mataimakin Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, a ranar Litinin, 16 ga watan Yuni.

Yawancin waɗanda aka kama matasa ne ‘yan tsakanin shekaru 15 zuwa 39.

Ana zargin su da shiga harkar daba, faɗa a titi da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi.

‘Yansanda sun ce wannan samame wani ɓangare ne na ƙoƙarin da suke yi na daƙile daba da dawo da zaman lafiya a birnin Kano.

Kwamishinan ‘Yansandan ya ja kunnen jama’a ka da su riƙa ɗaukar makamai a yayin shagulgulan gargajiya kamar “Gangi”, ko kuma nuna makamai a shafukan sada zumunta kamar TikTok, Facebook, Instagram da X, domin hakan na jawo wa matasa sha’awar shiga ayyukan daba.

Sanarwar ta kuma yi gargaɗi ga iyaye, da kuma masu ƙera makamai cewa duk wanda aka samu yana ɓoye ko taimaka wa ‘yan daba, ko kuma yana ƙera makaman da ake amfani da su wajen tashin hankali, za a gudanar da bincike a kansa tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Next Post
Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun ‘Yan Bindiga

Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun 'Yan Bindiga

LABARAI MASU NASABA

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.