’Yansanda a Jihar Neja sun kama wasu mutane tara da ake zargi da ƙirƙirar garkuwa da kansu.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Satumba, 2025, lokacin da aka samu rahoton garkuwa da wani mutum a unguwar Mandela da ke Minna.
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
- Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Daga baya kuma aka samu kira daga wata lamba, tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan bakwak.
A ranar 3 ga watan Satumba, ’yansanda suka kama wani mutum mai suna Suleiman Dauda.
Bayan yi masa tambayoyi, an kuma kama wasu mutane takwas a unguwar Mandela.
A lokacin gudanar da bincike, an samu layin waya guda 21 da takardun rijistar layi guda 29 a wajen Suleiman, wanda ya ce yana harkar rijistar layin ne.
Ya amsa cewa shi ne ya bai wa waɗanda “aka sace” waya da lambar da aka yi amfani da ita wajen neman kuɗin fansa.
Binciken ya nuna cewa waɗannan mutanen suna cikin wani tsari na zamba wanda ake kira da Ponzi.
An kuma gano cewa ɗaya daga cikinsu ya haɗa baki da wanda aka ce an yi garkuwa da shi don su karɓi kuɗi daga sauran abokan harkarsu.
SP Abiodun ya ce bincike ana ci gaba da bincike domin kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, yayin da aka riga aka gurfanar da waɗanda aka kama a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp