Rundunar ’yansandan Jihar Filato, sun kama mutum biyu ɗauke da bindigogi uku ƙirar gida da kuma wasu alburusai.
Kakakin rundunar, Alfred Alabo, ya ce a ranar 4 ga watan Agusta, 2025, tawagar rundunar daga sashen Kaduna-Vom ta dakatar da wani matashi mai shekara 24 mai suna Mark Ibrahim Dalyop.
- Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
- 2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara
Ta ce an same shi da bindigogi biyu ƙirar gida a kan hanyar Vom zuwa Kuru.
A ranar 11 ga watan Agusta, 2025, ’yansanda daga sashen Nasarawa Gwong sun sake kama wani mai suna Moses Aliyu, mai shekara 26, bayan samun bayanan sirri.
An kama shi a wani kango a yankin Kwanga, inda aka gano bindiga ƙirar gida da harsashi guda ɗaya a tare da shi.
Dukkanin mutanen biyu na Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya gargaɗi masu aikata laifi su daina ko su bar jihar.
Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da masu laifi sun fuskanci hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp