Rundunar ‘yansandan Jihar Legas ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da aikata fashi da makami.
Wadanda ake zargin sun kware wajen kwasar dukiyar jama’ar da ba su ji ba gani ba a unguwar Ajegunle da Alaba-Rago.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Ya bayyana wadanda ake zargin da suna Chukwuemeka Emmanuel mai shekaru 21, Chukwuebuka Innocent mai shekaru 24, Umaru Isah mai shekara 21, Emmanuel Ita mai shekaru 19, Olayitan Ayinde mai shekaru 18 da kuma Moshood Ayinde mai shekaru 25.
Hundeyin ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan gudanar da bincike cikin gaggawa kan rahotannin ayyukan wadanda ake zargin a yankin.
“Wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri biyu ne, an kama su ne a yankuna daban-daban na jihar.
“Ana ci gaba da kokarin kama wasu ‘yan kungiyar da suka gudu da kuma kwato wasu makamai,” in ji shi.
Ya kara da cewa an kwato babur din TVS daya mara rajista, bindiga guda daya, waya kirar Infinix Note 7 daya da kuma Iphone 7 guda daya daga hannun wadanda ake zargin.
A cewarsa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya idan an kammala bincike.
Ya ce kwamishinan ‘yansanda, CP Idowu Owohunwa, ya bukaci jama’a da su gaggauta sanar da ‘yansanda abubuwan da ake zargin na faruwa a yankunansu don kawo karshen ayyukan bata gari.