Hedkwatar ‘Yansandan Jihar Yobe ta kama mutum hudu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar, bayan wani samame da aka gudanar kan masu aikata laifi.
A cewar sanarwar kakakin ‘yansanda, SP Dungus Abdulkarim, a daren Asabar, wannan kamen na nuna jajircewar rundunar wajen tabbatar da doka da oda.
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
Sanarwar ta kara da cewa, wannan kokari na daga cikin matakan dabarun da rundunar ta dauka domin kawar da aikata laifuka a jihar.
Ta bayyana cewa, “A cikin makon da ya gabata, rundunar ta kama mutum hudu bisa zargin aikata laifuka daban-daban a sassa daban-daban na jihar, baya ga wasu nasarorin da aka samu a baya a ofisoshin ‘yansanda na kananan hukumomi.”
Sanarwar ta ce a wani bangare, “A Nguru, an kama wasu mutum biyu, Jarma Hussaini Adam, mai shekaru 25, da Mohammed Abdusalam, mai shekaru 16, bisa zargin kai wa wani dan sanda hari wanda ke aiki a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya. A ranar 26 ga Satumba, 2025, an same shi CPL Amani Ali ba tare da hayyacinsa ba tare da jininsa yana zuba, kuma an sace bindigarsa.
An gudanar da wani samame na musamman wanda ya kai ga gano bindigar da kuma cafke wadanda ake zargin. Jami’in da ya jikkata yana karbar magani a halin yanzu.”
“A Damaturu, jami’an sashen A’ na Hedkwatar ‘Yansanda sun cafke Ibrahim Alhaji Ahmadu, mai shekaru 24, bisa zargin shiga gona da dabbobi da kuma yi wa wani manomi barazana da bindiga. An kwato bindiga mai kananan harsasai daga hannunsa. Rundunar ta jaddada cewa mallaka da amfani da makamai wajen tsoratar da fararen hula babban laifi ne.”
Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa, “A Potiskum, an kama Dahiru Ali, mai shekaru 19, bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara uku. Bincike ya gano cewa wanda ake zargin ya taba aikata irin wannan laifi a kan wata yarinya ‘yar shekara uku a unguwar guda. Ya amsa laifinsa, kuma bincike na ci gaba.”
Kwamishinan ‘Yansanda, Emmanuel Ado, ya yi karfafa suka kan wadannan laifuka, inda ya jaddada matsayin rundunar na rashin sassauci kan aikata miyagun laifuka. Ya gargadi masu aikata laifi da su daina, in ba haka ba za su fuskanci mataki mai tsauri, tare da rokon iyaye da masu kula da yara su “rika kula da ‘ya’yansu sosai domin kare su daga batattu.”
CP din ya kuma sake jaddada kiran da yake yi ga iyaye da masu kula da yara da su kara tsaurara kulawa kan ‘ya’yansu don kare su daga masu yi wa yara barna, tare da rokon jama’ar jihar da su ci gaba da ba wa ‘yansanda goyon baya ta hanyar ba da bayanai cikin lokaci don tabbatar da tsaro da aminci ga kowa a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp