Jami’an Rundunar ’Yansandan Nijeriya, sun kama tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado.
Rahotanni sun shaida cewa an kama shi ne a ofishinsa na aikin lauya da ke kan titin Zariya a Kano.
- Ta’addanci: Ko Matakan Shawo Kan Taɓarɓarewar Tsaro Za Su Yi Tasiri?
- Firaministan Sin Zai Gudanar Da Tattaunawa Ta “1+10” Da Shugabannin Manyan Hukumomin Tattalin Arziki Na Duniya
Wani makusancinsa ne, ya tabbatar wa manema labarai, inda ya bayyana cewa jami’an ’yansanda ne suka yi kamen.
ADVERTISEMENT
Majiyarmu ta samu labarin cewa ‘yansandan sun tasa ƙeyar Barista Muhuyi, ne bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yansanda, Kayode Egbetokun.
Sai dai zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton ba mu samu cikakkun bayani game da dalilan kama shi ba.














