Rundunar ’yansandan Jihar Adamawa, ta kama wani mutum mai suna Mohammed Umar bisa zarginsa da sanya kayan mata yana yawo a harabar cocin LCCN da ke Ngurore, a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.
Kakakin ’yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce an kama mutumin ne bayan wani mutum mai suna Sunday Andrawus ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Ngurore.
- Hajji: Kawo Yanzu An Kammala Jigilar Maniyyatan Jihohi 12 A Nijeriya – NAHCON
- Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi
Ana zargin mutumin da yin basaja kamar yana aiki a cocin ne, wanda hakan na iya zama barazana ga masu ibada.
Kwamishinan ’yansandan jihar, CP Dankombo Morris, ya umarci a miƙa batun ga Sashen Binciken Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Rundunar ’yansandan ta bayyana ƙudirinta na tabbatar da tsaro da zaman lafiya, tare da buƙatar jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abun zargi a kan lokaci.
SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp