Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kama wata mata da ake zargin tana safarar makamai da miyagun ƙwayoyi ga ‘yan ta’adda a Jihar Katsina.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Talata, an kama matar mai shekara 30 ne tun a watan Disamban 2024, inda aka same ta da harsasai 124 da aka ɓoye a wata jarka mai cin lita biyar.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Nacewa Ga Samun Ci Gaba Mai Inganci Yayin Ziyararsa A Guizhou
- Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya Su
Matar ta shaida wa ‘yansanda cewa wani mutum ne ya aike ta da makaman zuwa Katsina.
Bincike ya gano wasu da ke da alaƙa da lamarin, kuma an kama su.
A wani samame daban da aka yi a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2025, ‘yansanda sun kama wasu mutane uku da ake zargin suna safarar magungunan codeine da wasu ƙwayoyi zuwa ga ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram a Jihar Yobe.
Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka.
Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp